Wasiyar Da Uba Yakamata Yayima Dansa.

​Dr. Mansur SokotoDaga Littafin “Abokin Hira” na biyu (Wallafar Dr. Mansur

Sokoto):

WASIYYAR WANI BAWAN ALLAH GA DANSA:

Ya kai dana!

Ka sani cewa, watarana tsufa zai kama ni. Zan rika yin

abubuwa ba yadda aka saba ba. Ka sa hakuri sosai don ka

fahimce ni.

Ya kai dana!

Idan wancan lokacin ya zo hannuna zai kasa rike abinci, sai

yana zuba a kan tufafina. Zan kasa cire ma kaina tufafi bayan

na lalata su ballai in iya sanya wasu. Ka yi hakuri da ni. Ka

tuna lokacin da na yi koya maka abinda yanzu na kasa iyawa.

A wannan lokaci zan kasa yin tsafta yadda kake bukata. Kada

ka manta ni ne na koya maka yin tsafta da kwalliya da shafa

turare.

Kada ka yi dariya idan ka ga ina yin wauta, ko na kasa gane

abubuwa yadda ya kamata. Ka zama kai ne kwakwalwata da

idona da kunnuwana don in gane abubuwa.

Ka tuna cewa, ni na koya maka zaman duniya da yadda ake jin

dadin rayuwa. Don me ba za ka yi hakuri idan na bukaci

wannan koyarwar ka koya min ba?

Idan lokacin da nike fadi ya zo tunanina zai yi rauni,

kasusuwan jikina za su yi sanyi, harshena zai yi nauyi. A

lokacin kuma babu abinda nake so sai kusancinka da jin

duriyarka. Yi kokari ka taimaka min don biyan bukatata. Ko a

wannan lokacin na san abinda nike so a raina kodayake ba

lalle ne in iya fada maka ba.

Ya kai dana!

Idan kafafuna suka kasa dauka ta, ka tuna lokacin da na rika

daukar ka har hannayena su yi sanyi. Idan na so ka sauka sai

ka ce ba ka sauka. Ni kan yi ta rarrashinka a wancan lokaci

don in samu yardarka. Kada ka ji kunyar rika hannuna ko

runguma ni a wannan lokaci. Watarana kai ma za ka bukaci

mai yi ma ka haka.

Ya kai dana!

Idan na tsufa zan daina fahimtar al’amurran duniya yadda ya

kamata. Zan rika jiran mutuwa ne a kowane lokaci. Kada ka

gajiya wajen taimakona domin wata babbar kofar aljanna ce

Allah ya bude maka.

Ya kai dana!

Idan ka tuna wani laifina a gare ka, ka iya fahimtar cewa, ban

yi shi don in musguna maka, ko in ketace ka ba. Na yi ne don

in koya maka zaman duniya da yadda za ka zama cikakken

mutum. A yau babban abinda za ka yi min shi ne ka manta da

kurakuraina, ka yafe laifukana. Ina fatar Allah ya yafe naka

kurakurai, ya gafarta laifukkanka.

Ya kai dana!

A lokacin da mahaifiyarka ta haife ka, ni ne na runguma ka, na

kula ka, na dauki nauyin ka, na yi tarainiya da kai. Ka saka min

a lokacin tsufa gabanin mutuwa ta.

Daga karshe, ina sanar da kai cewa, da dai ba ni da farin cikin

da ya fi jin dadinka, da ganin farin cikinka da murmushinka.

Kada ka bari idan zan bar duniya in bar ta da bakin cikinka ko

bacin rai a kan ka.

Allah ya yi maka albarka, ya sa ka gama da ni lafiya, ka samu

wadatar arziki da jin dadin rayuwa.

Advertisements