Tunatarwa

🌴RUWA CIKIN CHOKALI YA’ISHI MAI HANKALI YASHA YAYI WANKA🌴Wani mutum yazo Gurin sayyidina aliyyu Bn Abi dalib (R A) sai yace dashi zan tambayeka akan wasu tambayoyi guda hudu 4 kabani amsarsu. Tambayoyin sune kamar haka; -1 yace menene wajibi me yafi zama wajibi.-2 menene akusa kuma me yafi kusantowa -3 menene abin mamaki meyafi bada mamaki.-4 menene yake wahalarwa kuma me yafi bada wahala”AMSA DAGA SAYYIDI ALI( R A) Sai yacemasa abinda yake dole shine biyayya ga Allah (SWA) Abinda yafi xama dole kuma barin sabawa Allah.2 yace abinda yake kusa shine ranar alqiyama Abinda yafi kusanci kuma shine mutuwa 3 yace abin mamaki kuma shine duniya Abinda yafi bada mamaki kuma shine son duniya.4 yace amma Abinda yake mai wahala shine qabari Abinda kuma yafi bada wahala shine Tafiya lahira Babu guzuri. Allah kasa muje Asa’a. Ya allah mai juyar da xuciya katabbatar da zukatanmu Akan Addininka. Ameen . Daure katurawa koda mutum 1 ne.
MATA 10 WAINDA ALLAH YA
TSINE MUSU: –
ﺍﻟﻮﺍﺷﻤﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺷﻤﺎﺕ
1. Mata masu
tsaga
fuskokinsu. –
ﺍﻟﻨﺎﻣﺼﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺘﻨﺼﻤﺎﺕ
2. Mata masu
aske gashin
gira. –
ﺍﻟﻤﺘﻔﻠﺠﺎﺕ
3. Mata masu
kankare hakori
(wushirya). –
ﺍﻟﻮﺍﺻﻠﺔ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺻﻠﺔ
4. Mai ‘karin
gashi da wadda
ake karamata
gashin. –
ﺍﻟﺘﻲ ﺳﺨﻂ ﻋﻠﻴﻬﺎ
ﺯﻭﺟﻬﺎ
5.Matar da
mijinta yayi
fushi da ita. –
ﺍﻟﻤﺘﺸﺒﻬﺎﺕ ﺑﺎﻟﺮﺟﺎﻝ
6. Mata masu
shigar maza. –
ﺯﻭﺍﺭﺍﺕ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ
7. Mata masu
yawan
ziyartar
kabur-bura
(makabarta).
– ﺍﻟﻨﺎﺋﺤﺎﺕ
8. Mata masu
kururuwa akan
mamaci. –
ﺍﻟﻤﺤﻠﻞ ﻟﻪ
9. Mata masu
auren kashe
wuta. –
ﻛﺎﺳﻴﺎﺕ ﻋﺎﺭﻳﺎﺕ
ﻣﺘﺒﺮﺟﺎﺕ
10. Mata masu
bayyana
tsiraicinsu.
Kada ku manta TSINUWA itace
nisanta daga
rahamar Allah!
ﻗﺎﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ” ﻳﺎ
ﻣﻌﺸﺮ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ
ﺗﺼﺪﻗﻦﻭﺃﻛﺜﺮﻥ ﻣﻦ
ﺍﻹﺳﺘﻐﻔﺎﺭﻓﺈﻧﻲ
ﺭﺃﻳﺘﻜﻦ ﺃﻛﺜﺮ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻨﺎﺭ ” ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ
Manzon Allah (SAW)
ya ce: ‘Yaku
taron mata! ku
yi sadaqa,
kuma ku yawaita neman
gafara.
(Istigfari)
domin lallai
ninagan ku
mafiya yawanku
‘yanwuta
ne.”Allah yakaremu. Send it to ur family n frndx

Assalamu alaikum. Manzon Allah (S.A.W) yace:kuyi kokarin danne abubuwa uku:

(1) fushi (2) Sha’awa (3) Maganganunku.

Ku himmatu danyin abubuwa 2:
(1) Ayyukan Alkhairi (2) Abokai nagari.

Kuci moriyar abubuwa 2:
(1) Lokaci (2) Karfi.

Ku nemi abubuwa 3:
(1) Gafaran Allah (2) ilmi (3) Hikima.

YA ALLAH KABAMU IKON KIYAYEWA.

Ba’a gajiya da aikin alkhairi. Daure turawa ‘yan uwa musulmi domin samun lada.
✅Duniyar da za’a barta; mai ya kawo hadama❓✅Rayuwar da zata kare; Ina wani farin ciki❓✅Ana sauraren mutuwa; ina wata walwala❓✅Jikin da zai zama gawa; mai ya jawo ‘dagawa❓✅Karshen da makomarsa kabari; mai zai sa alfahari❓✅Wanda duk ya manta da wadannan, a ina yabar hankalinsa❓✅Inkaturashi xuwa gah wani/group domin ‘yan uwanka sugani sukaru wace asara kayi?❓Allah ya sa mu dace, ameen.

TUNATARWA AMUSLINCI

Rayuwa Haske ce. Mutuwa kuma Aya ce. Arziki
jarrabawa ne. Talauci kuwa Misali ne. Hankali
Makaranta ne. Ilimi kuwa Jagora ne. Jahilci
kuwa Duhu ne. Duniya gida ce. Qabari Daki ne.
lahira kuwa matabbata ce. Kada mu manta fa
mu baki ne yanda muka zo haka zamu koma.
Ya Allah kasa mudace.

HIKIMA ZINARIYA

Mafi hankalin mutun shine wanda ya bar

duniya tun kafin ta bar shi,

kuma ya gyara kabarinsa tun kafin ya shiga

cikinsa;

kuma yaji tsoron “Allah” tun kafin ya hadu

da “SHI”;

kuma yayi sallah a cikin jama’a tun kafin su

sallace shi;

Sannan kuma ya yi wa kansa hisabi tun kafin

ayi masa,

Domin yau ranar aiki ce, ba hisabi ba, gobe kuwa

Hisabi ne Ba Aiki ba.

Allah Ya sa mu dace.

Flow this page if you have interest to help your religion 

WHERE IS MUSLIM UMMAH!!!!!

sulaimanbsani@gmail.com

KWADAITARWA AKAN YIN SALLAR NAFILA CIKIN DARE(QIYAMUL LAIL)


KWADAITARWA AKAN YIN SALLAR NAFILA CIKIN DARE(QIYAMUL LAIL).*▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
1-Annabi s.a.w yace:

(Mafi alkhairi da falalar Sallah bayan sallar Farillah,itace Sallar lafiyar cikin Dare).
@رواه مسلم (1163).

2-Manzon Allah s.a.w yace:

(Inayi maku wasiyya akan kuyi riko da Sallar cikin dare,domin Dhabi’ar mutanan kirkice ta wadanda suka zo kafinku,Kuma tana kusantar da ku zuwq ga Ubangijinku,kuma kankarar zunubaice agareku,kuma tana goge laifuka).
@حسنه الألباني في إرواء الغليل (452)

2-Annabi s.a.w yana cewa:

(Lallai acikin aljanna akwai wani kataferan Bene,ana ganin cikinsa daga waje,kuma ana ganin wajansa daga cikinsa,)sai wani Balaraban Kauye yace:

“Na wanene ya Manzon Allah??” Sai yace:

(Na wanda yake:

-Kyautata magana 

-Yake ciyar da abinci dan Allah 

-Kuma yake azumin Nafila

-kuma ya tashi yake sallar dare lokacin da mutane suke barci).
@حسنه الألباني في صحيح الترمذي 
TAYAR DA IYALI DAN YIN SALLAR DARE TARE YANA LADA MAI GIRMA
1-Daga Hindu Bintul Haris daga Ummu Salmata R.A Matar Annabi s.a.w tace:

“Wata rana Annabi s.a.w ya tashi cikin firgici acikin dare yana cewa:

•سُبحانَ اللهِ 

SUBHANALLAH

Wani Abune Allah ya saukar na Taskoki,wani abune Allah ya saukar na Fitina Wazai Tayar min da iyalina koda zasuyi Sallar nafila acikin dare,sau da dama mai tufafi anan duniya zai tashi marar tufafi a lahira). 
#صحيح البخاري ( ٧٠٦٩ ) ].
2-Annabi s.a.w yana cewa:

(Allah ya jikan bawan da ya tashi cikin dare sannan ya tayar da matarsa dan suyi Sallah acikin dare,idan taki tashi sai ya sanya mata ruwa a fuskarta dan ta tashi,kuma Allah ya jikan matar da ta tashi cikin dare sannan ya tayar da mijinta dan suyi Sallah acikin dare,idan yaki tashi sai ta sanya masa ruwa a fuskarta dan ya tashi)
@صححه الألباني في 

[📚 صحيح الجامع ( ٣٤٩٤ ) ].
3- 2-Annabi s.a.w yana cewa:

(Idan Namiji ya tashi cikin dare,sannan ya tada matarsa sukayi Sallar raka’a biyu na nafila acikin dare,za’a rubuta su cikin bayin Allah masu ambaton Allah mai yawa).
@صححه الألباني في صحيح ابن ماجة ( ١١٠٦ ) ].
Awata ruwayar yazo da wannan Lafizin:
(( مَن استَيقظَ مِن اللَّيلِ وأيقظَ امرأتَهُ فصلَّيا ركعتَينِ جميعًا ، كُتِبا مِن الذَّاكرينَ اللَّهَ كثيرًا والذَّاكراتِ )) . 

@صححه الالباني في صحيح أبي داود ( ١٤٥١ ) ].

Allah ya jikin wanda ya yada wannan alkhairi ga Al’umma.
Ya kuma sanya mu cikin bayinsa masu yawan ibadar dare da kyakkyawar niyya da Ikhlasy.

MUYI TAKA TSAN TSAN DA IRIN TASHOSHIN DA AMERICA KE DAUKAR NAUYIN SU A AREWACIN NAGERIYA.

GASKIYA DACI GARETA

Ina ma’abota kallon wannan tasha ta 

Arewa24, ina mai maku sallama irin ta

addinin muslunci. Assalamu alaikum. A

 matsayina na Musulmi, kuma ‘dan 

Nigeria kuma ‘dan Arewa, na zurfafa wani binci ke, (Domin ni mai sha’awar

 bincike ne akan duk abinda nake ko nake

so) wanda nake ganin yana da matukar

 muhimmancin dukkanin ma’abota kallon 

wannan tasha su amfana da sakamakon

 wannan bincike nawa. Amma yana da kyau akan duk wanda ya

karanta wannan rubutu nawa kada ya

yanke mun hukunci har sai ya karanta

 rubutun tun daga farko har karshensa. Na

 biyu kuma duk abinda na rubuta wanda 

mai karatu bai gamsu da shi ba, to kamin ya yanke mun hukuci ina rokon sa da yayi 

bincike, ko ya tambayi masana da yake 

ganin suna binciken ababen dake faruwa

 a duniyar yanzu, ko ma yayi amfani da

 kafar bincike ta internet domin binciken 

wannan jawabi nawa. Da fatar Allah ya shige mana gaba adukkanin ababen da

muka sani a fili, da kuma wadanda suke 

a ‘boye. Da farko ni mai sha’awar kallon 

wannan 

tasha ne ta Arewa24, sakamakon suna

 gudanar da shirye-shiryensu da harshen Hausa, kuma ni bahaushe ne. Haka zalika 

yanayin fitar da hotonsu acikin quality 

mai kyau, ya taimaka a wajen samun

 sha’awata a gidan tv, sai kuma wasu 

shirye-shiryen su. To amma ababe da

yawa suna daure mun kai, ganin yadda ake kashewa gidan Tv

 kudi masu yawa tare da daukar 

ma’aikata masu yawa, da gudanar da

 shirye-shirye masu yawa wadanda ke 

bukatar kudi da yawa kamin a hada su.

 Kuma duk ace gidan tv yana yada shirye- shiryensa kyauta, kuma babu wasu 

kamfanoni da ke daukar nauyin gidan tv, 

ga zun zurutun kudin albashi da ake

 fitarwa a duk kowane wata. Wannan

 shine dalili na farko da ya jawo hankali

na, na gudanar da wani gajeren binciki akan:

-Su waye ke daukar nauyin wannan gidan

Tv??
– Ko anan gaba gidan Tv zai koma na kudi

ne?? 

– Ko akwai wasu manufofi da sune 

dalilin kafa wannan gidan Tv??

 Ganin wasu shirye-shirye da suka ci karo 

da al’adun Hausawa da Addininsu, kamar

 shirin H Hip Hop, ko meye manufar ire-

iren wadannan shirye shirye?? Wannan 

sune kawai dalilina na gudanar da wannan bincike da nayi, kuma na

samu bayanai da suka gamsar dani, na

wa dannan tambayoyi. 

1. Mai karatu SHI

KO KA SAN CEWA 

Arewa24 gidan tv America ne, Karkashin 

kulawar Federal bureau of Investigation Washington.
2. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA

 wannan gida Tv an ware masa 

zunzurutun kudi har Dala Miliyan 60 ($

60m)
3. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA An gina wannan gidan Tv domin rikicin da

yake faruwa na BOKO HARAM. A tunanin

su wannan gidan Tv zai taimaka wajen

 dauke hankalin samari daga zurfafa ga 

Ilimin Addinin Islama wanda suke 

tunanin kan iya taimakawa wajen kirkiro kungiyoyi tare da mara masu baya iren-

iren BOKO HARAM. Ta hanyar kirkiro 

shirye-shirye irinsu H Hip Hop wanda ake 

tunanin zai yi korarin da kushe zafin kan 

addini ga matasa, Kamar shirin zauren 

malamai; wanda akoda yaushe yana Magana ne akan JAHADI, ta hanyar tara 

wasu malamai da basu yi fice a wannan

 yanki namu ba akan karantarwar addini. 

Amma suke kokarin bayar da ma’anar

 JAHADI a muslunci da kashe-kashen sa.
4. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA shirin DADIN KOWA babbar manufar shirin ita

ce; daga karshe a nuna yadda malaman 

Addini ke komawa ‘yan boko haram, tare

da amfani da matasa.
5. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA yana 

daya daga cikin manufar kafa wannan gidan Tv, daidaita matsayin Maza da Mata 

acikin al’ummar Arewa, ta hanyar amfani 

da shirye-shirye iri daban daban 

6. Mai

karatu SHI KO KA SAN CEWA 

dukkanin shirye-shiryen wannan gidan Tv

ana tace su ne kadai anan Nigeria (Shooting and Editing) Amma sai ankai su

 America ake sakasu a satellite (Airing)
7. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA wasu 

manufofin kafa wannan gidan Tv, ko

 ma’aikatan wannan gidan bazasu san su

ba a yanzu (Kasan cewar muna fama da rashin aikin yi sosai a wannan kasa, shi ke

sa ba wani cikakken bin cike da mutanen 

zasu yi a yanzu, su dai bukatarsu su samu

a ikin yi) Domin turawa sun yi nisa wajen 

boye manufarsu, sai tafiya tayi nisa sosai 

zasu rika fitowa a fili. 

8. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA Duk 

shirye-shiryen da kake gani a yanzu an

a shirya su ne domin jawo hankalin jama’a

ga wannan gidan Tv, amma cikakkiyar 

manufar sai nan gaba sosai zata yi tasiri!!

Mai karatu ba ina kokarin goyon bayan kafa kungiyoyi irinsu boko haram bane, 

sai dai ina tsoron, a tafi “gyaran gira a

tsone idanuwa” Sakamakon lalacewar 

tarbiyar da wasu daga cikin shirye-

shiryen su zai iya haifarwa, musammam H

 Hip Hop, wanda tun a yanzu ya fara daukar hankalin matasa da ‘ya’yanmu 

matuka. Mai karatu ina tsoron ire-iren 

wadannan 

gidajen Tv da America ke kafawa domin

 bincike na, na gano wasu da aka gina a 

wasu kasashen Africa dana labarawa wanda America tayi, na kuma samu

 bayanai na tasirinsu a wadannan

 kasashe, wajen kokarin sauya masu

 al’adu. Mai Karatu manufar wannan

 rubutu nawa 

shine, muyi taka tsan-tsan da wannan gidan Tv. Mu san ire-iren shirye-shiryen da

zamu bar ‘yan’yanmu suna kallo a 

wannan gidan Tv. Daga karshe mai 

karatu, ni da nake

 wannan rubutu dalibi ne a Jami’a bana da

wata manufa ta kushe wannan gidan Tv, domin kona kushe shi bani da wani da

zan gabatar maka a madadinsa, face nayi 

ne kawai domin fadakar da ‘yan uwa 

musulmi. Idan kuma akwai akasin haka

 to Allah na gani kuma zai saka masu. 

Amma dai kai kanka mai karatu kayi naka binciken, domin na tabbatar da

cewa wannan rubutu nawa ba zai jima

akan internet ba, zasu goge shi Domin

 Karin bayani mai karatu ya ziyarci

 wadannan 

pages din;
 http://www.ibtimes.com/arewa24us-launches-

nigerian-tv

http://www.premiumtimesng.com/tag/arewa24 

http://newsrescue.com/nwo-landed-nigeria-us-

sponsor

Islam In Nigeria

    Islam in Nigeria

Nigeria has one of the largest Muslim populations in West Africa, with the Pew Research Center estimating that it is between 48.5% (2010) and 50.4% (2009). The CIA estimates 50% while the BBC estimates slightly over 50% (2007). Muslims in Nigeria are predominantly Sunni in the

Maliki school, which is also the governing Sharia law.[ citation needed ] However, there is a significant

Shia minority, primarily in Kaduna , Kano , Katsina and Sokoto State ; (see Shia in Nigeria). A smaller minority follow the Ahmadiyya , a reformatory sect originating in 19th century India. In particular Pew Forum on religious diversity identifies 3% as Ahmadi Muslims and 12 percent as Shia Muslims.
History

Islam was first documented in Nigeria in the 9th century.[citation needed] Religious archives showed Islam had been adopted as the religion of the majority of the leading figures in the Borno Empire during the reign of Mai (king) Idris Alooma (1571–1603), although a large part of that country still adhered to traditional religions. Alooma furthered the cause of Islam in the country by introducing Islamic courts, establishing mosques, and setting up a hostel in Makkah , the Islamic pilgrimage destination, for Kanuris .[8] It had spread to the major cities of the northern part of the country by the 16th century, later moving into the countryside and towards the Middle Belt uplands. However, there are some claims for an earlier arrival. The Nigeria-born Muslim scholar Sheikh Dr. Abu-Abdullah Abdul-Fattah Adelabu has argued that Islam had reached Sub-Sahara Africa, including Nigeria, as early as the 1st century of Hijrah through Muslim traders and expeditions during the reign of the Arab conqueror, Uqba ibn al Nafia (622–683) whose Islamic conquests under the

Umayyad dynasty, in Amir Muavia and Yazid periods, spread all Northern Africa or the Maghrib Al-Arabi , including present-day Algeria , Tunisia,

Libya and Morocco . 

Wasiyar Da Uba Yakamata Yayima Dansa.

​Dr. Mansur SokotoDaga Littafin “Abokin Hira” na biyu (Wallafar Dr. Mansur

Sokoto):

WASIYYAR WANI BAWAN ALLAH GA DANSA:

Ya kai dana!

Ka sani cewa, watarana tsufa zai kama ni. Zan rika yin

abubuwa ba yadda aka saba ba. Ka sa hakuri sosai don ka

fahimce ni.

Ya kai dana!

Idan wancan lokacin ya zo hannuna zai kasa rike abinci, sai

yana zuba a kan tufafina. Zan kasa cire ma kaina tufafi bayan

na lalata su ballai in iya sanya wasu. Ka yi hakuri da ni. Ka

tuna lokacin da na yi koya maka abinda yanzu na kasa iyawa.

A wannan lokaci zan kasa yin tsafta yadda kake bukata. Kada

ka manta ni ne na koya maka yin tsafta da kwalliya da shafa

turare.

Kada ka yi dariya idan ka ga ina yin wauta, ko na kasa gane

abubuwa yadda ya kamata. Ka zama kai ne kwakwalwata da

idona da kunnuwana don in gane abubuwa.

Ka tuna cewa, ni na koya maka zaman duniya da yadda ake jin

dadin rayuwa. Don me ba za ka yi hakuri idan na bukaci

wannan koyarwar ka koya min ba?

Idan lokacin da nike fadi ya zo tunanina zai yi rauni,

kasusuwan jikina za su yi sanyi, harshena zai yi nauyi. A

lokacin kuma babu abinda nake so sai kusancinka da jin

duriyarka. Yi kokari ka taimaka min don biyan bukatata. Ko a

wannan lokacin na san abinda nike so a raina kodayake ba

lalle ne in iya fada maka ba.

Ya kai dana!

Idan kafafuna suka kasa dauka ta, ka tuna lokacin da na rika

daukar ka har hannayena su yi sanyi. Idan na so ka sauka sai

ka ce ba ka sauka. Ni kan yi ta rarrashinka a wancan lokaci

don in samu yardarka. Kada ka ji kunyar rika hannuna ko

runguma ni a wannan lokaci. Watarana kai ma za ka bukaci

mai yi ma ka haka.

Ya kai dana!

Idan na tsufa zan daina fahimtar al’amurran duniya yadda ya

kamata. Zan rika jiran mutuwa ne a kowane lokaci. Kada ka

gajiya wajen taimakona domin wata babbar kofar aljanna ce

Allah ya bude maka.

Ya kai dana!

Idan ka tuna wani laifina a gare ka, ka iya fahimtar cewa, ban

yi shi don in musguna maka, ko in ketace ka ba. Na yi ne don

in koya maka zaman duniya da yadda za ka zama cikakken

mutum. A yau babban abinda za ka yi min shi ne ka manta da

kurakuraina, ka yafe laifukana. Ina fatar Allah ya yafe naka

kurakurai, ya gafarta laifukkanka.

Ya kai dana!

A lokacin da mahaifiyarka ta haife ka, ni ne na runguma ka, na

kula ka, na dauki nauyin ka, na yi tarainiya da kai. Ka saka min

a lokacin tsufa gabanin mutuwa ta.

Daga karshe, ina sanar da kai cewa, da dai ba ni da farin cikin

da ya fi jin dadinka, da ganin farin cikinka da murmushinka.

Kada ka bari idan zan bar duniya in bar ta da bakin cikinka ko

bacin rai a kan ka.

Allah ya yi maka albarka, ya sa ka gama da ni lafiya, ka samu

wadatar arziki da jin dadin rayuwa.