TARIHIN SAHABBAI

TARIHIN SAHABBAI DAGA WANNAN WEBSITE MAI ALBARKA:B’Sani’s Website
TARIHIN MA’AWIYA
“SARKIN MUMINAI MU’AWIYYA BN ABI
SUFYAN [RA]” Ya Musulunta kafin Fathu Makkah ,amma ya
boye Musuluncin sa saboda tsoron
Mahaifinsa.
Mu’awiyya na daya daga cikin sakatarori
[marubuta] na Annabi[SAW]masu rubuta
masa wahayi. Kai kasan koda a ma’aikatar ku akace wane sakatare ne to lalle yanada
daraja, balle Fada irinta Annabi[SAW]wadda
kaf duniya babu irinta.Ya kuma samu
kyakkyawar addu’a a dalilin kokarin sa inda
Annabi[SAW] ya roka Masa Allah ya sanya
shi shiryayye mai shiryarwa. Mu’awiyya na daga cikin mayakan Hunaini
wanda Allah ya shede su da imani kuma ya
ba da sanarwar saukar da nutsuwa a kansu
a cikin Taubah 91. Yana kuma cikin mutanen
da Allah ya yi wa alkawarin Al Husna wadda
itace Aljanna saboda sun ciyar da dukiya saboda Allah bayan cin garin Makka. Ya
kuma samu martabar kasancewa shugaba na
farko da ya kaddamar da Jihadi a teku, kuma
Annabi [SAW] ya yabama wadanda zasu yi
yaki a teku, yayi murna da Allah yanuna
masa su zazzaune kamar sarakuna a kan gadaje.

JARUNTAKA DA SARAUTA A RAYUWAR
MU’AWIYAH [RA]” Bayan Musuluntar Mahaifinsa Abu Sufyan
iyalan gidansu sunyi hijira tare dashi zuwa
Madina wurin Annabi [SAW]. Don haka
Mu’awiyah ya samu halartar sauran yake-
yaken da suka biyo baya.
Game da sha’anin sarauta Mu’awiyah ya dade da tunaninta a ransa tun ranar da Annabi
[SAW] ya ce masa, ya kai Mu’awiyah! Idan ka
Jibinci wani Al’amari kaji tsoron Allah kuma
kayi adalci.
Mutum na farko daya gabatar da Mu’awiyah
a sha’anin Mulki shine Khalifa Abubakar Siddik a lokacin daya shugabantar dashi akan
wata runduna da zata kai gudummawa ga
dan uwan sa Yazid, daya daga cikin jagorori
4 da suke yaki a kasar Sham.
Mu’awiyah ya cigaba da yaki a karkashin
tutar dan uwansa in da bajintar sa tasa aka rinka shugabantar dashi akan kananan
rundunoni yana cin nasara. Daga baya a
zamanin sarkin Musulmi Umar Bn Khaddab
aka ba Yazidu umarni ya shugabantar da
kanin nasa don cin garin kaisariyyah, ya tafi
kuma Allah yabashi nasara a can.

AYYUKAN SA A ZAMANIN SARAUTAR SA
SARKIN MUMINAI MU’AWIYAH [RA]” Sarkin Musulmi Mu’awiyah ya kula sosai da
sha’anin tsaro a kasar musulunci, shine
shugaba na farko a musulunci da ya fara sa
matsara a dalilin yunkurin kisansa da
khawarij sukayi. Yakuma kafa ma’aikatu da
dama don cimma wannan manufa. A dalilin haka gwamnatinsa ta samu karfinda yasa
tazamo babbar barazana ga duk sauran
al’ummai na duniya a wannan lokaci.
Sannan shi ya fara kafa ma’aikatar kula da
wasikun Sarki don gudun kar a sauya su.
Haka kuma Mu’awiya ya kula da sha’anin ilimi da jin dadin Malamai. A kan haka ne ya
kafa cibiyar nazari da fassara wadda aka
bata suna Baitul Hikmah. Ya kuma mayar da
hankali ga inganta rayuwar talaka. Haka
kuma ya mayar da hidimar alhazai kyauta.
A zamanin sa ne kuma yasa akayi magudanan ruwa a Madina, abinda yakawo
karshen matsalar cushewar ruwa
musamman a lokacin damina a cikin garin
Madina a wancan lokaci.
Copied by:basheerjournalistsharfadi.xtgem.com/Sahabbai

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s