YADDA AKE RAGE WUYAN TAGGUWA/RIGA

Aslm alkm
Dan uwana barka da zuwa wannan shafi nawa.
Yau kuma wata fasaha ce da wasu dubaru nawa da nai sha’awar rubutawa domin ‘yan’uwana masu irin sana’ata su fahimci abinda ya dade yana basu wahala to ga mafita.

Dan uwa Wannan fasahar cike take da sauki sai dai tunanin hakan bakowane zai iya hakaito hakan ba aransa, domin natanbayi wadansu daga cikin wadanda suka kware a wannan fannin sana’ar amma ban samu amsar da tai dai dai da irin wannan fasahar ba, domin kowanen su amsar da zai bada tana zammtowa gurguwar amsa saboda dole sai amma tagguwar/rigar illa, ko tarage tsawo ko wuyan yaki fita yadda ake bukatar shi.
Hakan naga yadace da in bayyanama masu irin wannan sana’ar tawa abin da na fahimta dangane da ita wannan sana’a.
Ta iya yuwar cewa bani ne nafara fahimtar hakaba wani ya rigani fahimtar haka, falillahil hamdu. Amma shi wanda yafahimci hakan tuntuni kafinni ba wata kila bai irin wannan gamsashshen bayanin ba, imma dai yayi duk falillahil hamdu fatana dai, shine Allah yafahimtar da wadan da basu fahimci kan ba.
Abin da yasa nai wannan jawabin nasan mu teloli munada kuri, wani da yaji wannan jawabin nawa, sai yace yaro ka makaro kai sai yanzun ma kasan haka, to ni ba irin wannan telan bane ni duk abin da bansani ba tanbaya nake inkuma nasani sonike wani yasani yakuma kara zurfafa tunanin shi sama da nawa akan haka, ALLAH KAI MANA JAGORA.

YADDA WANNAN FASAHA TAKE
Dan uwana wanda wuyan riga/tagguwar ka kafiddashi sama da kima ma’ana yaima yawa, to ga hanyar da zaka bi domin ka magance matsalarka.

Kasami zare da allura kasan ya wa allurar ka ta hannu zaren da ka ke amfani dashi akan wannan dinkin,sai ka linka zaren linki biyu yadda zai isheka kazagayo wuyan batare da ya kare ba, sai ka daure kasan zaren sannan sai ka tsiro allurar ka daga tsagar da zaka fidda kwalar wuyan ka ma’ana farko wuya kenan,
Sai ka rinka nitsar da allurar ka kana fiddo da ita kuma kana bada ‘yattazara atsakani tamkar dai yadda kifi ke tsalle sai kuma ya nitse acikin teku, sai kuma can gaba yakara tsalle kuma sai yanutse acikin ta, to haka allurar ka zata kasan ce tamkar kifi, yadinka kuma tamkar tekun da wannan kifi ya ke nutso acikinta,sannan dinkin ka ya karance gefen wuyanka ma’ana kusa da karshen wuya. Idan ka kai karshe ma’ana kenan yanzun ka zagaye wuyan ka da wannan zaran.
In mai sauraro yana biyedani acan baya nace ya kulle zaran sa, kuma zare yakasance linki biyu, amfani hakan shine kullin zaren ka ninki biyu shine zai iya hana zaren ka wucewa cikin yadin amma in dayane to zai iya wucewa.
Anan gabar nake cewa kai da kazagaye wuyan ka da zare yadda nace, to sai ka kama wannan zaren sai ka rinka zugeshi ahankali kuma kana yi kana jan zugewar agaba har karshe zaka ga ko ina yadan tattare karkadamu da wannan, ka’auna yadda kake bukatar wuyan da tape in yayi kadan sai ka kara sassauta zugewar, inkuma yayi yawa sai ka kara zugewar yadda kake bukata.
Mai sauraro acan baya nacema kada kadamu da tattarewar da zaiyi domin duk irin wuyan da zaka dora guru ne ko higher neck ne dadai sauransu to zai hana wannan tattarewar tafito bayan ka dora shi.
ALLAH YA TEMAKEMU AMEEN.

To mai sauraro anan wannan dan jawabin nawa yakare fatana shine wanda bai sani ba yasani.
ALLAH YAI MANA JAGORA.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s