MUYI TAKA TSAN TSAN DA IRIN TASHOSHIN DA AMERICA KE DAUKAR NAUYIN SU A AREWACIN NAGERIYA.

GASKIYA DACI GARETA

Ina ma’abota kallon wannan tasha ta 

Arewa24, ina mai maku sallama irin ta

addinin muslunci. Assalamu alaikum. A

 matsayina na Musulmi, kuma ‘dan 

Nigeria kuma ‘dan Arewa, na zurfafa wani binci ke, (Domin ni mai sha’awar

 bincike ne akan duk abinda nake ko nake

so) wanda nake ganin yana da matukar

 muhimmancin dukkanin ma’abota kallon 

wannan tasha su amfana da sakamakon

 wannan bincike nawa. Amma yana da kyau akan duk wanda ya

karanta wannan rubutu nawa kada ya

yanke mun hukunci har sai ya karanta

 rubutun tun daga farko har karshensa. Na

 biyu kuma duk abinda na rubuta wanda 

mai karatu bai gamsu da shi ba, to kamin ya yanke mun hukuci ina rokon sa da yayi 

bincike, ko ya tambayi masana da yake 

ganin suna binciken ababen dake faruwa

 a duniyar yanzu, ko ma yayi amfani da

 kafar bincike ta internet domin binciken 

wannan jawabi nawa. Da fatar Allah ya shige mana gaba adukkanin ababen da

muka sani a fili, da kuma wadanda suke 

a ‘boye. Da farko ni mai sha’awar kallon 

wannan 

tasha ne ta Arewa24, sakamakon suna

 gudanar da shirye-shiryensu da harshen Hausa, kuma ni bahaushe ne. Haka zalika 

yanayin fitar da hotonsu acikin quality 

mai kyau, ya taimaka a wajen samun

 sha’awata a gidan tv, sai kuma wasu 

shirye-shiryen su. To amma ababe da

yawa suna daure mun kai, ganin yadda ake kashewa gidan Tv

 kudi masu yawa tare da daukar 

ma’aikata masu yawa, da gudanar da

 shirye-shirye masu yawa wadanda ke 

bukatar kudi da yawa kamin a hada su.

 Kuma duk ace gidan tv yana yada shirye- shiryensa kyauta, kuma babu wasu 

kamfanoni da ke daukar nauyin gidan tv, 

ga zun zurutun kudin albashi da ake

 fitarwa a duk kowane wata. Wannan

 shine dalili na farko da ya jawo hankali

na, na gudanar da wani gajeren binciki akan:

-Su waye ke daukar nauyin wannan gidan

Tv??
– Ko anan gaba gidan Tv zai koma na kudi

ne?? 

– Ko akwai wasu manufofi da sune 

dalilin kafa wannan gidan Tv??

 Ganin wasu shirye-shirye da suka ci karo 

da al’adun Hausawa da Addininsu, kamar

 shirin H Hip Hop, ko meye manufar ire-

iren wadannan shirye shirye?? Wannan 

sune kawai dalilina na gudanar da wannan bincike da nayi, kuma na

samu bayanai da suka gamsar dani, na

wa dannan tambayoyi. 

1. Mai karatu SHI

KO KA SAN CEWA 

Arewa24 gidan tv America ne, Karkashin 

kulawar Federal bureau of Investigation Washington.
2. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA

 wannan gida Tv an ware masa 

zunzurutun kudi har Dala Miliyan 60 ($

60m)
3. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA An gina wannan gidan Tv domin rikicin da

yake faruwa na BOKO HARAM. A tunanin

su wannan gidan Tv zai taimaka wajen

 dauke hankalin samari daga zurfafa ga 

Ilimin Addinin Islama wanda suke 

tunanin kan iya taimakawa wajen kirkiro kungiyoyi tare da mara masu baya iren-

iren BOKO HARAM. Ta hanyar kirkiro 

shirye-shirye irinsu H Hip Hop wanda ake 

tunanin zai yi korarin da kushe zafin kan 

addini ga matasa, Kamar shirin zauren 

malamai; wanda akoda yaushe yana Magana ne akan JAHADI, ta hanyar tara 

wasu malamai da basu yi fice a wannan

 yanki namu ba akan karantarwar addini. 

Amma suke kokarin bayar da ma’anar

 JAHADI a muslunci da kashe-kashen sa.
4. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA shirin DADIN KOWA babbar manufar shirin ita

ce; daga karshe a nuna yadda malaman 

Addini ke komawa ‘yan boko haram, tare

da amfani da matasa.
5. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA yana 

daya daga cikin manufar kafa wannan gidan Tv, daidaita matsayin Maza da Mata 

acikin al’ummar Arewa, ta hanyar amfani 

da shirye-shirye iri daban daban 

6. Mai

karatu SHI KO KA SAN CEWA 

dukkanin shirye-shiryen wannan gidan Tv

ana tace su ne kadai anan Nigeria (Shooting and Editing) Amma sai ankai su

 America ake sakasu a satellite (Airing)
7. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA wasu 

manufofin kafa wannan gidan Tv, ko

 ma’aikatan wannan gidan bazasu san su

ba a yanzu (Kasan cewar muna fama da rashin aikin yi sosai a wannan kasa, shi ke

sa ba wani cikakken bin cike da mutanen 

zasu yi a yanzu, su dai bukatarsu su samu

a ikin yi) Domin turawa sun yi nisa wajen 

boye manufarsu, sai tafiya tayi nisa sosai 

zasu rika fitowa a fili. 

8. Mai karatu SHI KO KA SAN CEWA Duk 

shirye-shiryen da kake gani a yanzu an

a shirya su ne domin jawo hankalin jama’a

ga wannan gidan Tv, amma cikakkiyar 

manufar sai nan gaba sosai zata yi tasiri!!

Mai karatu ba ina kokarin goyon bayan kafa kungiyoyi irinsu boko haram bane, 

sai dai ina tsoron, a tafi “gyaran gira a

tsone idanuwa” Sakamakon lalacewar 

tarbiyar da wasu daga cikin shirye-

shiryen su zai iya haifarwa, musammam H

 Hip Hop, wanda tun a yanzu ya fara daukar hankalin matasa da ‘ya’yanmu 

matuka. Mai karatu ina tsoron ire-iren 

wadannan 

gidajen Tv da America ke kafawa domin

 bincike na, na gano wasu da aka gina a 

wasu kasashen Africa dana labarawa wanda America tayi, na kuma samu

 bayanai na tasirinsu a wadannan

 kasashe, wajen kokarin sauya masu

 al’adu. Mai Karatu manufar wannan

 rubutu nawa 

shine, muyi taka tsan-tsan da wannan gidan Tv. Mu san ire-iren shirye-shiryen da

zamu bar ‘yan’yanmu suna kallo a 

wannan gidan Tv. Daga karshe mai 

karatu, ni da nake

 wannan rubutu dalibi ne a Jami’a bana da

wata manufa ta kushe wannan gidan Tv, domin kona kushe shi bani da wani da

zan gabatar maka a madadinsa, face nayi 

ne kawai domin fadakar da ‘yan uwa 

musulmi. Idan kuma akwai akasin haka

 to Allah na gani kuma zai saka masu. 

Amma dai kai kanka mai karatu kayi naka binciken, domin na tabbatar da

cewa wannan rubutu nawa ba zai jima

akan internet ba, zasu goge shi Domin

 Karin bayani mai karatu ya ziyarci

 wadannan 

pages din;
 http://www.ibtimes.com/arewa24us-launches-

nigerian-tv

http://www.premiumtimesng.com/tag/arewa24 

http://newsrescue.com/nwo-landed-nigeria-us-

sponsor

Advertisements

4 thoughts on “MUYI TAKA TSAN TSAN DA IRIN TASHOSHIN DA AMERICA KE DAUKAR NAUYIN SU A AREWACIN NAGERIYA.

 1. B. Ssni duck abinda ka fada gaskiya ne. Allah ya saka da alkhari. Amin. Sai dai maganar wai suna kawo malaman da basusan komai akan jihadi ba to anan ni ina ganin akwai gyara a wannan bigire. Domin dukkan malaman nan munsansu kwarai da gaske. Saidai kawai maiyiwuwa fahimtar da suka yiwa jihadi ya bambanta da naka. Kuma dai mu da ba malamai ba mun San cewa mutum yadau makami yayi ta kashe wadda bai jiba bai gani ba wai da sunan jihadi. Kuma yawancin yakin da annabi(SAW) yayi sai an tabo shi. Kuma baya shiga gari yayi ta kashe mutane ba dalili. Kaskiya mu yan arewa maso gabas munji dadin bayanin da kayi akan arewa24 amma fa batun jihadi irin na boko haram fa mun dan tsorata da bayayanimka. Domin malaman da kake magana akansu kokari suke su nunawa mutane cewa kashe mutane ba dalili ba shine jihadi irin Wanda manzon Allah yayi back
  Wassalamu alaikum.

  Like

 2. Fatana shine, muyi taka tsan-tsan da wannan gidan Tv. domin Mu san ire-iren shirye-shiryen da
  zamu bar ‘yan’yanmu suna kallo a
  wannan gidan Tv.
  Allah kaimana Jagora
  Ameen

  Like

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s